Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Domin girmama shahidan Iran shugaban kasar Iran da kuma ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sauran shahidan da suka yi hadarin jirgin sama, an sauke tutar Majalisar Dinkin Duniya zuwa rabi kuma an sauke tutocin kasashe mambobin Majalisar dake hedkwatar wannan Majalisar zuwa kasa gaba ɗaya.
